ABNA24 : Kungiyoyin fara hula da dama a kasar sun kudiri anniyar shigar da karar gwamnati da kuma kamfanonin sadarwa na kasar game da toshe intanet, yau kusan kwana goma.
Matakin dai a cewar kungiyyin ya sabawa ‘yancin da kowa yake da shi na sanin halin da duniya ke ciki.
Da yammacin ranar 23 ga watan Fabarairu da ya gabata ne aka katse kafar intanet a kasar ta Nijar, bayan rikicin da ya biyo bayan sanar da sakamakon zaben shugabancin kasar zagaye na biyu, wanda dan takaran jam’iyya mai mulki ya yi nasara a cewar fa hukumar zaben kasar ta CENI.
Masana da dama na danganta toshe hanyoyin na intanet da abun takaici wanda tuni ya haifar da illa ga harkokin jam’ar kasar nay au da kulun, yayin da kasashen duniya sukayi gum da bakunansu kan lamarin.
Babban Dan takaran adawa na kasar Alhaji Mahamane Usman, ya wallafa a shafinsa na twitter, cewa matakin katse intanet din wani yunkuri na toshe yancin fadar albarkacin baki.
342/